Dan bindigar da ya so kashe tsohon shugaban ƙasar Trump ya yi gaban kansa ne – FBI

0 249

Hukumar tsaro ta FBI a Amurka ta ce ɗanbindigar da ya so kashe tsohon shugaban ƙasar Trump ya yi gaban kansa ne wajen kai harin, ba wai yana aiki ne da wasu ba.

Ta ce ya sayi irin zungureriyar bindigar nan ce mai sarrafa kanta da ake kira AR 15 domin aiwatar da shirin nasa.

FBI ta ƙara da cewa an sayi bindigar ne bisa doka kuma an gan shi rataye da ita lokacin da aka harbo shi daga saman rufin benen da ya yi harbin.

Matashi ne mai shekara 20 da ake kira Thomas Matthew Crooks.

Hukumar ta kuma ce an gano wasu bama-bamai a cikin motar wanda ake zargin, kodayake har yanzu ba a fayyace dalilinsa ba, ko wata akida, ko ma taɓin hankali da suka ingiza shi aiwatar da shirin nasa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: