Labarai

Dan takarar gwamnan jihar Jigawa a jam’iyar PDP Mustapha Lamido ya taya gwamnan jihar Delta murna bisa zabar sa da aka yi a matsayin mataimakin Atiku Abubakar

Dan Takarar Gwamnan Jihar Jigawa karkashin tutar Jam’iyar PDP Mustapha Sule Lamido, wanda aka fi sani da Santuraki, ya taya Gwamnan Jihar Delta Ifeanyi Okowa, murna bisa zabar sa da aka yi a matsayin mataimakin Atiku Abubakar.

Santuraki, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa, bayan Atiku Abubakar, ya zabi Okowa a matsayin wanda zai masa takarar mataimakin shugaban kasa a Jam’iyar PDP.

A cewarsa, zabar Okowa a matsayin mataimakin Atiku babbar nasara ce ga Jam’iyar PDP musamman a zaben 2023 wanda yake karatowa, biyo bayan gogewarsa da kuma gudunmawar da zai bawa Jam’iyar.

Haka kuma ya bukaci yayan Jam’iyar ta PDP da yan Najeriya su marawa Jam’iyar PDP baya domin kaiwa ga nasara.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: