Dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu, ya ce ba za a zargi matasan Najeriya da kasala ko lalaci ba

0 56

Dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu, ya ce ba za a zargi matasan Najeriya da kasala ba.

Tinubu ya yi ikirarin cewa matasan Najeriya ba za a zarge su da zama cima zaune ba idan akayi la’akari da rashin samar da wutar lantarki da ake fuskanta a kasa.

Da yake jawabi ga matasan jam’iyyar APC, jiya a jihar Legas, shugaban jam’iyyar na kasa, ya ce Najeriya ba za ta iya samun ci gaba cikin sauri ba tare da wutar lantarki ba.

Ya ci gaba da cewa Najeriya ba za ta iya ci gaba da bayar da uzuri na rashin samar da ingantaccen wutar lantarki ba.

Idan dai za’a iya tinawa Shugaba Muhammadu Buhari a watan Afrilun 2018, ya bayyana matasan Najeriya a matsayin malalata cima zaune.

Ya ce galibin matasan Najeriya suna son zama ba tare assala aikin komai ba, tare da ikirarin cewa Najeriya kasa ce mai arzikin man fetur.

Ana dai ganin kamalam na Bola Ahmad Tinubu a matsayin kalaman siyasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: