Dangote na fuskantar ƙalubale daga wasu manyan ‘yan kasuwar man fetur

0 46

Masana’antar sarrafa mai mallakin shahararren dan kasuwar nan Alhaji Aliko Dangote na fuskantar ƙalubale daga wasu manyan ‘yan kasuwar man fetur da ke ƙin sayen kayayyakin man daga matatar Dangote, duk da ƙara yawan fitar da kayayyaki da ta ke yi.

Dangote ya bayyana cewa tun kafin a fara cikakken aiki da matatar, ya bayyana cewa akwai wadanda suke ƙoƙarin ganin ma’aikatar ta gaza, ta hanyar hana ta isasshen ɗanyen mai da kuma jinkirta sayen kayayyakin ta.

Sai dai sabanin hakan, bayanan hukumar NMDPRA sun nuna cewa shigo da fetur daga ƙasashen waje ya ragu daga lita miliyan 44.6 a kullum a watan Agustan 2024 zuwa lita miliyan 14.7 a watan Afrilu da ya gabata, abin da ke nuna ci gaba daga matatar Dangote da sauran matatun cikin gida.

Dangote ya ce duk da irin ƙoƙarin da ake yi don rushe masa masana’antar, yana da tabbacin zai yi nasara a ƙarshe, yana mai cewa Najeriya da Afirka gaba ɗaya na buƙatar irin wannan muhimmin aiyyukan.

Leave a Reply