Daruruwan mutane sun bar gidajensu bayan an kai hari a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo

0 76

Daruruwan mutane ne suka bar gidajensu bayan wasu mutane dauke da makamai sun kai hari a kauyukan gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo.

Mazauna yankin sun ce maharan sun fatattaki wasu tsirarun sojojin kasar domin mamaye wasu kauyukan lardin North Kivu.

Wata kungiyar farar hula a daya daga cikin kauyukan ta ce tana zargin maharan ‘yan tawaye ne.

Kungiyar ‘yan tawayen, wacce ta kulla yarjejeniya a shekarar 2013 da gwamnati don kawo karshen tawaye, ba ta ce uffan ba kan harin.

A baya-bayan nan ne ayyukan ‘yan tawaye suka girgiza wasu sassan lardunan South Kivu da North Kivu, kuma lardin North Kivu na karkashin mamayar sojoji domin dakile hare-haren ‘yan tawaye.

A makon da ya gabata ‘yan tawaye sun kai hari tare da tsayar da komai a garin Bukavu da ke North Kivu na tsawon sa’o’i.

Leave a Reply

%d bloggers like this: