Labarai

‘Dauk wadanda suka zarge ni da nuna son kai a siyasar jihar Jigawa suna da ‘yancin bin hanyarsu ta siyasa a wasu jam’iyyun” – Sule Lamido

‘Dauk wadanda suka zarge ni da nuna son kai a siyasar jihar Jigawa suna da ‘yancin bin hanyarsu ta siyasa a wasu jam’iyyun” – Sule Lamido——–
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas a matsayin mutum mai rikon dattako wanda yake da dabi’u irin na matasa.
A wata zantawa da ya yi da Sashen Hausa na BBC, Sule Lamido ya ce wasu ne ke tunzura gwamnan ya yiwa jam’iyyarsa bore.

Sule Lamido ya roki Nyesom Wike ya kasance mai tawali’u kuma ya koyi darasi daga Peter Obi da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.Ya kara da cewa zaben Osun ya nunawa ‘yan Najeriya inda nasara take.
Dan siyasar jamhuriya ta biyu ya ci gaba da cewa wadanda suka zarge shi da nuna son kai a siyasar jihar Jigawa suna da ‘yancin bin hanyarsu ta siyasa a wasu jam’iyyun.
Ya yi mamakin dalilin da ya sa wasu ke jin haushinsa saboda goyon bayan dansa Mustapha Sule Lamido a takararsa ta gwamna.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: