Ministan Ayyuka kuma tsohon Gwamnan Ebonyi, David Umahi, ya musanta ƙoƙarin da wasu ke yi na haɗa kawunan ‘yan adawa domin kawar da Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa ba su da wani karfi ko inganci.
A wata hira da ya yi da Musulmai yayin Sallar Layya a Abakaliki, Umahi ya jaddada yadda gwamnatin Tinubu ke bai wa Kudu maso Gabas kulawa ta musamman, inda ya ce an ba yankin manyan mukamai fiye da yadda aka saba.
Ya roƙi ‘yan kabilar Igbo da su goyi bayan gwamnatin Tinubu, yana mai cewa jituwa tsakanin addinai da haɗin kan siyasa suna da matuƙar muhimmanci a ci gaban ƙasa.
Umahi ya kuma ambaci ziyarar Tinubu zuwa Vatican a matsayin alamar fahimtar addinai da zaman lafiya, yana mai kira da a bar rigima a rungumi cigaba.