Sanata Ibrahim Shekarau ya karbi katin zama dan NNPP.

Sanatan wanda aka zabe shi a matsayin sanata a karkashin jam’iyyar APC ya fice daga jam’iyyar ne biyo bayan rikici mai tsanani.

Da yawa daga cikin magoya bayansa sun shaida yadda aka sauya shekar a fadar Mundubawa ta Ibrahim Shekarau.

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda ya halarci taron sauya shekar a hukumance ya mikawa Ibrahim Shekarau katin zama dan jam’iyyar NNPP

Wadanda suka halarci taron sun hada da masu ruwa da tsaki na siyasa da magoya bayansa a bangaren Kwankwasiyya da shugabannin majalisar Shura ta gidan Ibrahim Shekarau da sauran masu hannu da shuni.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: