Dole a karɓi allurar Korona ko mu rike albashi a cewar ƙaramar hukumar Garki dake jihar Jigawa

0 108

Karamar hukumar Garki dake nan jiharnan ta umarci dukkanin ma’aikatan karamar hukumar akan su karbi alluarar rigakafin cutar corona ko kuma su rikewa ma’aikaci albashi.

Shugaban karamar hukumar Alh. Mudasir Musa ne ya bayar da wannan umarnin, a lokacin dayake kaddamar da yaki da cutar covid-19 a sakatariyar karamar hukumar.

A cewar sa babu wani ma’aikacin karamar hukumar da zai samu albashin watan Disamba, harsai ya gabatar da katin shedar karbar allurar rigakafin.

Ya kara da cewa bukatar hakan ta zama dole ne, bisa kudirin gwamnati na yaki da wannan cutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: