Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun rufe cibiyar matasa ta Sani Abacha, inda aka yi shirin gudanar da taron tsagin jam’iyyar APC a jihar Kano.

Jami’an tsaron, wadanda suka kori ‘yan jarida a kofar shiga cibiyar, sun ce an ba su umarnin kwace wajen tare da dakatar da duk wani taro.

Sun ce an sanar da su cewa wajen da aka amince da babban taron jam’iyyar APC na jihar shine fili wasanni na Sani Abacha.

Tun da farko a filin wasannin, Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya ayyana duk wani taron wani tsagin jam’iyyar a matsayin haramtacce.

Kazalika, jami’an tsaro sun harba hayaki mai sa hawaye da yawa don tarwatsa mutanen da suka taru a Cibiyar Matasan ta Sani Abacha, dake kan hanyar Madobi a birnin Kano.

An harba hayaki mai sa hawayen zuwa daya daga cikin shagunan da ke kallon cibiyar inda wasu magoya bayan suka nemi mafaka.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: