Duk Ƴan PDP Su Kwantar Da Hankalinsu, Zamu Yi Nasara – Secondus

0 379

Jam’iyyar PDP mai adawa ta yi kira ga shugabanni da sauran ya’yan jamiyyar da su kwantar da hankalinsu, sakamakon abinda ya faru dangane da karar da jam’iyyar ta shigar kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa na 2019.

Shugaban kwamittiin yan jam’iyyar Sanata Walid Jubrin ya bayyana hakan yayin wani taron shugabannin kwamittin gudanarwa na jamiyyar karo 86 da aka yi a helkwatar jamiyyar ta kasa dake Abuja.

Ya ce jam’iyyar PDP za ta sake shugabanci a Najeriya nan gaba.Shugaban jamiyyar na kasa Mr. Uche Secondus ya ce nasarorin da jamiyyar ta samu a zaben gwamnoni wani zakaran gwajin dafi ne na cewa nan gaba akwai nasara.

Kazalika Scondus ya ce jamiyyar da sauran magoya bayanta da sauran lauyoyinta a shirye suke su kwato yancinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: