Duk dan takarar da ya fi dacewa da Najeriya shi zan goyawa baya a shekarar 2023 – Sule Lamido

0 67

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce zai goyi bayan duk wani dan takarar shugaban kasa da ya fi dacewa da kasar nan a shekarar 2023.

Sule Lamido ya bayyana haka ne a jiya yayin wata hira da gidan talabijin na Channels.

Da aka tambaye shi ko jiga-jigan Arewa sun yanke shawarar cewa yankin zai fitar da shugaban kasa, tsohon gwamnan bai amsa tambayar ba.

Maimakon haka, ya ce bai yarda da hadin kai na yanki ko na kabilanci ba.

Sule Lamido, jigo a jam’iyyar PDP, ya bayyana damuwarsa da cewa duk kokarin da aka yi a baya na tabbatar da zaman lafiya a kasarnan, an ruga shi a ‘yan kwanakin nan, sakamakon karuwar rikice-rikicen kabilanci da na addini.

Da yake mayar da martani kan sanarwar da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi na shiga takarar karbar mulki daga hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023, tsohon gwamnan ya yi imanin cewa Tambuwal na daya daga cikin wadanda suka fi cancanta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: