Labarai

Duk kalubalen dake addabar Najeriya, ciki har da rashin tsaro, an gaje su ne daga tsohuwar gwamnatin da ta gabata – Gwamna Badaru

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, yace kalubalen dake addabar kasarnan, ciki har da rashin tsaro, an gaje su ne daga tsohuwar gwamnatin da ta gabata.

Gwamnan yace gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samu gagarumin cigaba a fannoni da dama, musamman a bangaren gine-gine.

Gwamna Badaru yayi Magana a jiya wajen bikin cika shekaru 60 da kafa kungiyar zabi son ka ta kasa a Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

Yace akwai bukatar ‘yan Najeriya su kasance masu hakuri da yawaita adduo’i domin kawo karshen kalubalen rayuwa da na tattalin arzikin dake addabar kasarnan.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: