EFCC Ta Kama Mutane 11 Kan Zargin Damfara Ta Intanet

0 64

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta kama wasu mutane 11 da ake zargin suna damfarar ta intanet a kananan hukumomin Jere da Maiduguri a jihar Borno.

Kakakin hukumar Wilson Uwujaren ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar jiya Laraba a Abuja.

Ya ce wadanda ake zargin da aka kama a ranar Laraba sun hada da Olatunji Sherif, Bright Felix, Jude Magaji, Jonah Jondi, Ojobaro Abdullahi, Jerry Zizighi da Micah Joseph.

Sauran sun hada da Mari Ayuba, Ibrahim Abdullahi, Adam Abiodun da kuma Victor Chinonso Okolieaboh.

Uwujaren ya ce an kama su ne a wani samame da aka kai bayan sahihan bayanan sirri kan ayyukan da ake zarginsu da aikatawa.

Za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike.

NAN

Leave a Reply

%d bloggers like this: