EFCC ta kama tsohon babban jami’in kuɗi na NNPCL bisa zargin wawure $7.2Bn

0 154

Hukumar EFCC ta kama tsohon babban jami’in kuɗi na kamfanin man fetur na kasa NNPCL, Umar Isa, da tsohon darektan matatar man Warri, Jimoh Olasunkanmi, bisa zargin wawure dala biliyan 7.2 da aka ware don gyaran matatun man.

Kama su na cikin binciken da ake ci gaba da yi kan yadda aka yi amfani da kudin da aka ware wa gyaran matatun Kaduna, Warri da kuma Fatakwal.

Wani kwamitin majalisar dattawa da Sanata Aliyu Wadada ke jagoranta ya nuna damuwa kan gibin bayanai a lissafin kuɗin NNPCL daga 2017 zuwa 2023.

Hukumar na duba zarge-zargen almundahana, cuɗanya da kwangiloli da kuma barnatar da dukiyar al’umma.

Leave a Reply