Hukumar EFCC ta ce a shekarar 2024 ta samu nasarar da ba ta taɓa samu ba tun da lokacin da aka ƙirƙire ta.
Ta ce a shekarar ta ƙwato kuɗaɗe da suka haɗa da naira biliyan 364.6 da dala miliyan 214.5 da fan 54,318.64 da yuro 31,265 da kuɗin ƙasar Canda, dala 2,990 sai kuma kuɗin ƙasar Australia, dala 740, kamar yadda ta bayyana.
Hukumar ta ƙara da cewa a shekarar ce ta ƙwato rukunin gidaje 750, wanda shi ne mafi girma a tarihin hukumar.
Haka kuma ta ƙwato kuɗaɗen kirifto irin su Bitcoin da Ethereum da USDT masu darajar miliyoyin daloli da sauransu.
Hukumar ta kuma ƙwato kamfani da otel da zinare da fulotai.
Hukumar ta ce ta samu ƙorafe-ƙorafe guda 15,725, ta gurfanar da mutane aƙalla 5,083 a kotu, ta samu nasara a shari’a guda 4,011.
Rahoton da hukumar ta fitar ya nuna cewa ta samu wannan nasarar ce ta hanyar aiki da jajircewar jami’anta wajen yaƙi da almundahana da sauran laifuka a ƙasar baki ɗaya.