EFCC Tace Ta Kama Mutane 12 Bisa Zargin Sayen Kuri’u Jiya A Kano Da Katsina.

0 64

Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati EFCC tace ta kama mutane 12 bisa zargin sayen kuri’u a zabukan cike gibi da aka gudanar jiya a jihohin Kano da Katsina.
Kwamandan EFCC na shiyyar Kano, Faruk Dogondaji, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa yayin wata ganawa cewa an kama wadanda ake zargin dauke da kudi naira miliyan 1 da rabi a jihohin Kano da Katsina.
A cewarsa, an kama mutane 10 a karamar hukumar Doguwa ta jihar Kano, yayin da aka kama mutane 2 a karamar hukumar Kankiya ta jihar Katsina.
Faruk Dogondaji yace an kama wadanda ake zargin lokacin da suke kokarin sayen kuri’un masu zabe da kudi a wasu akwatunan zabe.
Yace samun ma’aikatan hukumar ta EFCC a guraren zabe ya kara sahihancin zabukan.
Kwamandan na EFCC yace za a gurfanar da wadanda ake zargi a kotuna da zarar an kammala bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: