Reshen Ofishin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ƙasa EFCC ta damke wasu yan asalin ƙasar China su biyu bisa tayin bayar da cin hanci ga daya daga cikin babban jami’in hukumar a Sokoto.

Yan China da aka kama masu suna Mr. Meng Wei Kun da kuma Mr. Xu Koi sun kwadaitawa Shugaban shiyyar hukumar reshen jihar sokoto Malam Abdullahi Lawal da zunzurutun kudi har Naira miliyan Ɗari. 

Hukumar dai ta kame yan kasar China ne su biyu  jiya Litinin 11/05/2020 

yan China sun yi kokarin bayar da cin hancin ne a wani yunkurin dakatar da bincike kan wata badakalar kwangila da aka bayar a jihar Sokoto ga wani kamfani mai suna Zhonghao Nig. Ltd, da gwamnatin jihar Zamfara ta bawa kwangila tsakanin shekarun 2012 zuwa 2019 da kudin kwangilar ya kai har N50,000,000,000.00 (Naira Billiyan 50)

Ofishin shiyyar na kan binciken kamfanin ne bisa kwangilar gina titunan cikin garuruwan Gummi, Bukkuyun, Anka da Nassarawa na jihar ta Zamfara;

Da kuma wasu aiyukan samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana da burtsatsai ta samar da ruwan sha a kananan hukumomi 14.

Saboda dakile yunkurin hukumar ne bayan da suka ga lallai asirinsu zai toni, sai suka yi yunkurin bawa babban jami’in hukumar cin hanci don a bar maganar ta wuce idan har ya yarda zasu biya N100,000,000 miliyan Ɗari.

Saboda jami’in yana son kama su a hannu sai ya dana musu tarko.

A jiya wakilan kamfanin suka je don a binne binciken, Meng Wei Kun da kuma Xu Kuoi suka kawo Naira miliyan 50 kafin alkalami, da zummar cikon zai biyo baya idan bukata ta biya.

Bayan zuwan su ne da kudin sai nan take jami’an hukumar EFCC suka cafke su da kudin a tare da su don ya zama shaida.

Kawo yanzu bincike ya nuna cewa kamfanin Zounghao Ltd Ya karbi makudan kudi har N41,000,000,000.00 (Naira Biliyan Arba’in)  Daga gwamnatin jihar Zamfara.

Kuma kusan N16,000,000,000.00 (Naira Biliyan Goma sha shida) ya tafi a almubazzaranci ne an karkatar da shi ta wata hanyar wanda bincike ke nuna zuwa wurin yan chanjin kudaden kasar waje ake kaiwa.

Yan China biyun da ake zargi nan gaba kadan za’a gurfanar da su gaban kuliya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: