Kwanaki kadan kafin karewar wa’adin mulkinsa, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya amince da tsige sarakunan Piriga da Arak, Jonathan Paragua Zamuna da Aliyu Iliyah Yammah.
Wata sanarwa da kwamishiniyar kananan hukumomin Umma Ahmad ta sanyawa hannu, ta ce tsige sarakunan biyu ta fara aiki daga jiya.
A cewar sanarwar, Hakimin Garun Kurama, Babangida Sule, shi ne zai kula da harkokin masarautar Piriga, har zuwa lokacin da za a nada sabon sarki, yayin da aka umarci sakataren majalisar masarautar da ya kaddamar da aikin nadin sabon sarki.
Sakataren majalisar masarautar Arak, Gomna Ahmadu, shi ne zai kula da al’amuran masarautar tare da kaddamar da tsarin nada sabon sarki. Sanarwar ta kuma sanar da sallamar hakiman kauyukan Aban, Abujan Mada da Anjil da ke masarautar Arak ba tare da bata lokaci ba.