Fadar shugaban ƙasa ta ƙaryata zargin da ake na rashin jituwar da ke tsakanin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima, inda ta bayyana cewa dangantakar shugabannin biyu na nan da ƙarfinta.
Babban mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa ga mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwar da ya fitar a bikin cikar mataimakin shugaban ƙasar shekaru 58.
Nkwocha ya bayyana zargin a matsayin “makirci mara tushe.
Sanarwar ta jaddada cewa Shettima wani muhimmin ɓangare ne na gwamnatin Tinubu inda yake bai wa shubgaban kasar cikakken goyon baya da kuma ƙwarin gwiwa.
Ya bayyana kwazon Shettima da jajircewarsa ga shugaba Tinubu, inda ya bayyana cewa biyayyar mataimakin shugaban ƙasa da hadin gwiwarsu sun taimaka wajen samun kyakkyawan yanayi da hadin kai a cikin gwamnatin.
A ƙarshe ya jaddada irin gudummawar da Shettima ke bai wa gwamnatin Tinubu, inda ya nuna cewa mataimakin Shugaban kasar ya kawo wani nau’i na kwarewa da kuzari na musamman don tallafa wa manufofin gwamnati.