Fadar Shugaban kasa ta gorantawa masu cewa su kaɗai suka ɗora Buhari kan karagar mulki

0 166

Fadar Shugaban Najeriya ta ce babu wanda ya isa ya ce shi kaɗai ya yi uwa ya yi makarɓiya har Shugaba Muhammadu Buhari ya hau kan karagar mulki a zaɓen 2015.

Mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ne ya fitar da sanarwa inda ya ce abin da ya wuce a baya bai kamata ya zama abin da za a yi la’akari da shi ba a wurin zaɓen da ke tafe.

Ya bayyana cewa abin da ke da muhimmanci a yanzu shi ne a zaɓi shugaba da zai kawo ci gaba a Najeriya.

Ya bayyana cewa akwai waɗanda suka ba shugaban shawara da ya ƙara takara da waɗanda suka gina jam’iyya inda ya ce babu wani mutum guda da zai iya cewa shi ya yi duka waɗannan shi kaɗai.

Sai dai ana ganin wannan sanarwar da Fadar Shugaban Najeriyar ta fitar ba ta rasa nasaba da wasu kalamai da Bola Ahmed Tinubu ya yi masu kama da gori inda ya ce shi ya taimaka Buhari ya ci zaɓe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: