Farfesa Yemi Osinbajo ya ce har yanzu mutane na kashe kudade masu yawa wajen neman lafiya a Najeriya

0 44

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ce har yanzu mutane na kashe kudade masu yawa wajen neman lafiya a Najeriya duk da dumbin kasafin kudin da ake warewa bangaren kiwon lafiya a duk shekara.

Yemi Osinbajo ya bayyana hakan ne a jiya a jawabinsa na musamman a taron kaddamar da rahotannin manufofin ci gaba mai dorewa a Najeriya.

An gudanar da taron ne a dakin taro na fadar shugaban kasa dake Abuja.

Yemi Osinbajo ya ce tilas ne Najeriya ta dinke barakar da ke tsakanin kasafin kudin kiwon lafiya da kuma kudaden da mutane ke kashewa wajen neman lafiya a kasarnan.

Mataimakin shugaban kasar ya ce rahotannin sun kawo karshen wani dogon aiki da aka fara a watan Disambar 2018 a taron karawa juna sani na yankin Afirka kan muradun ci gaba mai dorewa a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

Yemi Osinbajo ya bayyana cewa, tare da amincewa da ajanda da tsare-tsaren ci gaba mai dorewa, Najeriya ta shigar da kanta cikin wani shiri na kawo karshen talauci da kuma bayar da gudunmawa wajen kare duniya nan da shekarar 2030.

Leave a Reply

%d bloggers like this: