Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya yi kira da a samar da kyakkyawar fahimtar juna tsakanin masu fada aji da tsarin siyasar da zai inganta hadin kan al’umma a kasarnan.
Yemi Osinbajo ya yi wannan kiran ne a jiya a wajen taron lacca akan Tsare-tsare da Gudanar da Mulki da Cibiyar Nazarin Dabaru ta Kasa da ke Kuru, kusa da Jos ta shirya.
Ya kafe kan cewa kamata yayi bambancin mu ya zama alkhairi ba sharri ba, inda ya kara da cewa Najeriya na da damar zama kasa mai girma amma sai an yi yaki da annobar rarrabuwar kawuna.
Yemi Osinbajo, wanda ya buga misali da kasashen Singapore, Tanzania da Ruwanda, a matsayin kasashen da suka gudanar da harkokinsu yadda ya kamata, ya ce Najeriya za ta iya koyi da su.
Akan matsalar ‘yan asalin jiha da baki, mataimakin shugaban kasar ya yi kira da a sauya takardar shaidar kasancewa dan jiha zuwa takarar zama ko ta haihuwa, yana mai jaddada cewa irin wannan matakin zai inganta hadin kai.
Tun da farko, Darakta Janar na Cibiyar, Farfesa Ayo Omotayo, ya gode wa mataimakin shugaban kasa bisa amsa gayyatar da cibiyar ta yi masa na gabatar da lacca.
- Comments
- Facebook Comments