Fasinjojin motocin sufuri ne suke bayyana damuwarsu kan abun da suka kira rijiya ta ba da ruwa guga ta hana, da masu motocin haya ke musu, ta hanyar ƙin rage farashin sufuri.
Sun ce ya kamata a rage kuɗin sufuri saboda raguwar da aka samu a farashin litar man fetur.
Fasinjojin sun koka kan yadda suka ce hakan na shafar ɓangarorin rayuwarsu da dama, musamman tafiye-tafiye zuwa wuraren sana’a ko kasuwanci.
Sai dai direbobin sun ce har yanzu farashin bai daidaita ba ne, inda suka yi alƙawarin da zarar farashin ya daidaita za su yi wani abu.
A ranar Larabar da ta gabata ne dai matatar man fetur ta Dangote ta sake rage farashi man daga naira 890 zuwa naira 825, sannan kamfanin NNPCL shi me ya bi sahu, abin da ake ganin wani matakin samun sauƙi ne ga ƴan ƙasa.