Fiye da fararen hula 30 aka kashe biyo bayan tashin hankalin da ya barke a kasar Sudan ta Kudu

0 66

Fiye da fararen hula 30 aka kashe jiya biyo bayan tashin hankalin da ya barke tsakanin kabilu biyu a jihar Warrap da ke tsakiyar kasar Sudan ta Kudu.

Jihar Warrap ita ce mahaifar shugaban kasar, Salva Kiir.

An samu tashin hankali a wurare da dama a jihar, ciki har da lardunan Tonj-North da Tonj-East, wadanda a baya-bayan nan aka yi ta samun rikici.

Ministan yada labarai na jihar Warrap, Ring Deng ya shaidawa manema labarai cewa mutane 29 sun jikkata a rikicin da ya shafi al’ummomin makwabta uku.

Ya alakanta musabbabin tashin hankulan da satar shanu.

Ring Deng ya ce ana cigaba da kokarin karfafa tsaro a yankunan da ba su da kwanciyar hankali domin shawo kan lamarin da ke tabarbarewa cikin sauri.

Leave a Reply

%d bloggers like this: