Gamayyar jam’iyyun siyasa ƙarƙashin jagorancin African Democratic Congress (ADC) ta sanar da sabon wuri domin ƙaddamar da sabon taronta
Gamayyar jam’iyyun siyasa ƙarƙashin jagorancin African Democratic Congress (ADC) ta sanar da sabon wuri domin ƙaddamar da sabon dandalin siyasarta, bayan da Wells Carlton Hotel ta soke masauƙin taron kwatsam a safiyar Laraba.
A cikin wata sanarwa da Mataimakin Sakataren na Ƙasa Jami’iyyar ADC, Nkem Ukandu, ya sanya wa hannu, gamayyar ta bayyana cewa ƙaddamarwar za ta gudana yanzu a Cibiyar Shehu Musa Yar’Adua da ke Abuja da ƙarfe 2:00 na rana a ranar Laraba.
Soke taron ya tayar da ƙura a tsakanin shugabannin jam’iyyun adawa, inda wasu ke zargin gwamnatin APC da tsoma baki a harkokin siyasarta.
