Labarai

Gamayyar kungiyoyin mata 229 sun yi Allah-wadai da Majalisun kasarnan kan kin amincewa da duk wani kudirin doka da ya shafi mata

Gamayyar kungiyoyin mata 229 sun yi Allah-wadai da Majalisun kasarnan kan kin amincewa da duk wani kudirin doka da ya shafi mata, yayin kada kuri’a kan gyaran kundin tsarin mulkin kasarnan na shekarar 1999 da aka yi jiya.

Kungiyoyin, a cikin wata sanarwa, sun bayyana cewa abin bakin ciki ne matakin da ‘yan majalisar suka dauka na hana mata karin dama da samun wakilci a harkokin Mulki.

A cewarsu majalisun sun yi magana da babbar murya cewa ba sa son cigaban iyayensu mata da ’yan uwansu mata da kuma ‘ya’yansu mata.

Daga cikin kudirori 68, kimanin kudirori biyar ne suka nemi inganta karin damarmaki ga mata a jam’iyyun siyasa, mulki da kuma al’umma baki daya kuma anyi watsi da dukkanninsu.

A wata sanarwa da kungiyoyin matan suka fitar ga manema labarai sun ce ‘yan majalisar sun zabi tauye mata hakkin mata. Kungiyoyin sun kuma shirya gudanar da zanga-zanga a zauren majalisar a yau domin neman biyan bukatunsu.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: