Garken giwaye sun yi mummunar barna a tsakiyar kasar Mozambik inda suka lalata gidaje da rumbunan abinci da kuma amfanin gona

0 110

Garken giwaye sun yi mummunar barna a tsakiyar kasar Mozambik inda suka lalata gidaje da rumbunan abinci da kuma amfanin gona.

Jami’ai a lardin Safala na kasar sun ce dabbobin na bukatar ruwa domin guraren samun ruwan su na yau da kullum sun kafe.

Sun ce giwayen sun yi ta lalata duk wani abu da ke kan hanyarsu, kuma wasu iyalai sun bar gidajensu sun koma wani waje.

Rikicin giwaye na dada karuwa a kasar Mozambik kuma suna barin wuraren da ake killace su domin neman abinci da ruwa.

Hukumar kula da muhalli ta kasar ta ce namun daji sun kashe kusan mutane 100 a cikin shekaru biyun da suka gabata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: