General Yakubu Gowon yace duk da irin kiyayyar da aka nunawa NYSC, shine abu mai kyau da ya faru a Najeriya.

0 277

Tsohon Shugaban Kasar Najeriya na Mulkin Soja, General Yakubu Gowon, ya bayyana cewa duk da irin kiyayyar da aka nunawa Shirin Yiwa Kasa Hidima NYSC a lokacin Kafashi, har yanzu yana daga cikin abubuwa masu kyau da suka faru a Najeriya.

General Yakubu Gowon shine Shugaban Kasar da ya kafa Hukumar Yiwa Kasa Hidima NYSC, domin a samu hadar hada kan yan Kasa.

Tsohon Shugaban Kasar ya bayyana hakan ne a lokacin da ake kaddamar da wani Littafi da hukumar NYSC ta rubuta domin bikin tunawa da kafuwar hukumar shekaru 48 da suke wuce.

Gwamnan Jihar Nasarawa Engineer Abdullahi Sule, shine ya kaddamar da littafin, a taron da hukumar ta shirya wanda ya samu halartar Shugaban Hukumar Shu’aibu Ibrahim da Shugaban Kwamatin Cigaban Matasa na Majalisar Wakilai Mista Yemi Adaramodu da sauran su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: