Kwamitin yaki da Ambaliyar ruwa na jihar Kaduna ya bayyana yin gine-gine ba tare da izini ba da kuma zubar da shara a magudanun ruwa a matsayin manya daga cikin abubuwan da ke haifar da yawaitar ambaliya da sauran ibtila’in muhalli a jihar.
Kwamitin, karkashin jagorancin Shugaban ma’aikatan jihar, Liman Sani Kila, ya ce, dole ne mazauna jihar su daina aikata wadannan ayyukan domin kawo karshen ambaliyar ruwa ta dindindin.
A kwanakin baya ne hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kaduna, KADSEMA ta bayyana cewa, fiye da gidaje 2000 ne ambaliyar ruwa ta shafa a kananan hukumomin Zariya da Sabon Gari da ke jihar kadai.
Dangane da haka ne Gwamna Uba Sani ya kafa kwamitin domin tantance irin barnar da ambaliyar ruwa ta yi a garin Muchia da karamar hukumar Sabon Gari da sauran wurare a jihar, tare da gano abubuwan da ke sanya yankunan ke fama da matsalar. Shugaban kwamatin, ya bayar da tabbacin cewa, Gwamnan ya kuduri aniyar daukar matakan da za su magance matsalar ambaliyar ruwa domin hana afkuwarsa a nan gaba.