Gogaggun yan bindiga sun harbe wani ɗan sanda a Jihar Ondo

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashi ne sun harbe wani jami’in ɗan sandan Najeriya a Jihar Ondo da ke kudancin ƙasar.
Kakakin ‘yan sanda a Ondo, DSP Funmilayo Odunlami, ta shaida wa kafar talabijin ta Channels TV ranar Talata cewa lamarin ya faru ne a Oka-Akoko na Ƙaramar Hukumar Akoko ta Yamma.
Mazauna yankin sun shiga ruɗani sakamakon faruwar lamarin da tsakar ranar Talata bayan maharan sun isa a babura, inda suka harbe ɗan sandan kuma suka ƙara gaba.
Ta ƙara da cewa tuni suka ƙaddamar da bincike don gano waɗanda suka aikata kisan.
An kai gawar jami’in wanda ba a bayyana sunansa ba mutuware na wani asibiti da ke kusa.
Asalin Labarin: BBCHausa