Gwaman jihar Kogi ya bayyana cewa itace jihar da tafi kowacce tsaro a Najeriya

0 96

Gwaman jihar Kogi Yahaya Bello ya bayyana cewa jihar kogi ce mafi tsaro domin zama da kuma gudanar d harkokin kasuwanci a Arewacin kasar nan.

Yayin dayake jawabi Sanata Smart Adeyemi a babban birnin tarayya ne ya bayyana hakan, a lokacin daya wakilci gwamnan jihar.

Ya kara da cewa, jihar itace wajan da kowa zai gudanar da harkokinsa batare da kalubalen rashin tsaro ba, ya kuma bukaci  masu zuba jari daga kasashen duniya akan su gaggauta zuba jari a jihar.

Ya kuma bukaci matasan kasar nan su karbi takarar Yahaya Bello a matsayin dan takarar shugbaancin kasar nan a zaben 2023.

A madadin gwamnan Adeyemi ya kaddamar da fara gangamin yakin neman zaben Yahaya Bello a zaben 2023.

Leave a Reply

%d bloggers like this: