Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya kaddamar da Ofishin Matarsa a Kano

0 70

Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya kaddamar da Ofishin Matarsa a Jihar, wanda hakan yana daga cikin kudurin gwamnatinsa na ganin cewa ana damawa da Mata a harkokin Gwamnati.

A cewarsa, an bude Ofishin ne saboda da kokarin da Farfesa Hafsat Abdullahi Ganduje take yi domin ciyar da Matan Jihar gaba ta fannin samar musu da hanyoyin dogaro da kai.

Haka kuma ya ce Matar tasa, ta taka muhimmiyar rawa wajen nadin Kamsiloli Mata a kananan hukumomi 44 da kuma masu bawa Shugabannin Kananan Hukumomi Shawara duk domin a rinka damawa da Mata a cikin harkokin gwamnati.

A jawabansu Kwamishiniyar Ma’aikatar Mata Dr Zahara’u Umar Muhammad, da Shugabar Ma’aikata ta Jiha Hajiya Binta Lawan da kuma Shugabar Matan Jam’iyar APC ta shiyar Arewa Maso Yamma Hajiya Yahanasu Buba sun yabawa Gwamna Ganduje bisa samar da Ofishin.

Daruruwan Mata ne da kuma Kungiyoyin Mata suka halarci taron domin taya Matar Gwamnan Murna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: