Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar Jigawa ya amince da kafa kwamitocin gudanarwa na manyan makarantu hudu dake jiharnan.

Makarantun sune kwalejin ilimi ta Gumel da kwalejin ilimi da shari’ah ta Ringim da makarantar fasahar sadarwa ta informatics dake Kazaure da kwalejin share fagen shiga jami’a dake Babura.

A wani cigaban mai alaka da wannan, Gwamnan ya kuma amince da nada Alhaji Habu Isyaku, Durbin Ringim, a matsayin shugaban hukumar bayar da tallafin karatu ta jiha.

A wani labarin, Gwamna Badaru ya amince da nadin Dr. Hussaini Shehu, a matsayin shugaban kwalejin share fagen shiga jami’a dake Babura.

Kazalika, Gwamnan ya kuma amince da nadin Rabi’u Saleh Kazaure a matsayin magatakardar kwalejin.

Dukkan nade-naden na kunshe cikin sanarwa daban-daban dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jiha, Alhaji Adamu Abdulkadir Fanini.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: