Labarai

Gwamna Badaru Abubakar ya amince da sake nadin Farfesa Babawuro Usman a matsayin shugaban makarantar Informatics Kazaure.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya amince da sake nadin Farfesa Babawuro Usman a matsayin shugaban makarantar fashaar sadarwa ta zamani dake Kazaure a sabon wa’adin tsawon shekaru hudu.

Sanarwar da babban sakataren maaikatar ilmi ta jiha Umar Sule Gwaram ya fitar tace sake nadin ya fara aiki ranar 1 ga watan da muke ciki.

Sanarwar ta taya shugaban murnar sake nadin nasa tare da bukatar zai kara kwazo da himma wajen ciyar da makarantar gaba.

A wani labarin kuma, sashen bada horo da jagoranci na ofishin shugaban ma’aikata na jiha ya umarci matasan da aka dauka aiki a matsayin sojan sama ‘yan Jigawa dasu hallara a hukumar bada guraben ilmi ta jiha dake Dutse a gobe lahadi, domin daukarsu zuwa Kaduna.

A sanarwar da daraktan sashen Ibrahim Abdullahi Ringim ya fitar, ta bukaci matasan dasu tabbatar sun hallara da misalin karfe 7 da rabi na safe domin tafiya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: