Gwamna Badaru ne ya maida jihar Jigawa sabuwar duniya cikin shekaru shida – Ahmad Lawan

0 91

Shugaban majalissaar dattawa ta kasa Sanata Ahmed Lawan ya jinjinawa al’ummar jihar jigawa da gwamantin jiharnan murnar samun nasarorin gudanar da ayyukan cigaban jiha, da kuma kammala manyan ayyuka a fadin jihar nan.

Lawan ya bayyana hakan ne a lokacin dayake ganawa da masu ruwa da tsaki da kuma deligates na jam’iyyar APC a birnin Dutse.

Kafin hakan Ahmed Lawan yana daya daga cikin masu neman jam’iyyar APC ta tsaida shi a matsayin dan takarar jam’iyyar APC a zaben shugbaan kasa, wanda za’a gudanar da zaben fidda gwani a karshen watan nan.

Lawan yace a matsayin sa na wanda yake makwabtaka da jihar Jigawa, yana ganin yanda cikin shekaru 6 gwamna Badaru ya kawo cigaba a fadin jihar.

Anasa jawabin gwamnan jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar yace, Ahmed Lawan dan’uwansa ne, kuma zasu yi kokarin ganin cewa, jam’iyyar APC ta tsayar da dan takarar da zai lashe babban zaben gama gari na kasa da za’agudanar a 2023.

Leave a Reply

%d bloggers like this: