Gwamna Badaru ya aike da sakon ta’aziyya ga Sarkin Hadejia bisa rasuwar Ambassada Daudu Suleiman

0 92

Gwamna jihar jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya aike da sakon taaziyya ga mai martaba Sarkin Hadejia kuma shugaban majalissar sarakunan jihar Jigawa Alhaji Dr Adamu Abubakar Maje CON bisa rasuwar tsohan jakadan Nigeria a kasar Korea ta Arewa Ambassada Daudu Suleiman.

Sakon taaziyar mai dauke da sa hannun mai baiwa gwamna shawara kan kafafan yada labarai da Hulda da jama-a Habibu Nuhu Kila, Gwamnan ya bayyana rasuwar marigayi a matsayin babban rashi ne ga iyalai da alummar jihar Jigawa da kuma kasa baki daya.


Gwamnan ya bayyana marigayi a matsayin dattijo wanda ya saudakar da rayuwarsa wajen yiwa alumma hidima.


Daga nan sai ya yi adduar Allah ya ji kansa ya kuma baiwa iyalai da yan uwa hakurin jure babban rashin da aka yi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: