A wani yunkurin nuna tausayawa da jin kai ga yan kasuwar garin Shuwarin, gwamnan jihar Jigawa Alh. Muhammad Badaru Abubakar ya yarda a dawo cin kasuwar mako-mako bayan da ya bayar da umarnin kulleta cikin makon nan.
Tun farko gwamnan ya sanya an kulle kasuwar ne saboda kin yin biyayya da dokokin matakan kariya daga annobar Korona da aka shinfida ga kowacce kasuwa a jihar.
Sai dai matar na tuba ba ta rasa miji, shugabannin yan kasuwar sun kaiwa gwamnan ziyara tare da alƙawarin bin dokoki matukar ya amince suka dawo hada-hadarsu.
Hakan ta sanya gwamna Badaru amincewa tare da yi musu gargadi a matsayin damar karshe gare su.
- An yiwa masu matsalar gani 161 tiyatar Yanar Ido kyauta a babban asibitin Hadejia
- An kama wani matashi bisa laifin bankawa kakarsa wuta
- Obasanjo ya nemi shugabanni suyi amfani da tarin albarkatu da Najeriya ke dashi domin ciyar da ita gaba
- APC ta shawarci Sanata Ali Ndume kan ya riƙa gabatar da ƙorafin sa kai tsaye ga Bola Tinubu
- An tsinci gawar ƙaramin yaro a ƙarƙashin Gadar Oyun
Babban Mataimaki na Musamman Ga Gwamnan Jihar Jigawa a kan Kafafan sadarwar zamani Auwal D Sankara, ya bayyana cewa gwamna Badaru ya fi bayar da fifiko kan lafiyar jama’arsa fiye da batun ribar kasuwanci.
Shugaban yan Kasuwar Alhaji Muhammad Adamu wanda ya samu jagorancin shugaban majalisar dokokin jihar Alhaji Idris Garba Jahun sun roki gwamnan da ya amince ya bawa yan kasuwar wata damar, sun yarda zasu bi duk ka’idodin da aka shinfida.
Shi ma shugaban karamar hukumar Kiyawa Malam Isyaku Adamu yayi gargadin cewa zasu dauki tsattsauran mataki kan duk wanda aka samu yaki bin dokar, domin shi da kansa zai jagoranci kwamitin da zai na kula da al’amuran kasuwannin.