Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na nan Jihar Jigawa ya bayyana cewa Gwamnatinsa ta cika Kaso 94.8 na Alkawarirrikan da ta dauka a Lokacin yakin neman Zabe.

Gwamna Badaru Abubakar, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar Lambar Girmamawa daga Kungiyar Hadejia Ina Mafita.

A cewarsa, mutanen yankin Masarautar Hadejia sun bukaci ayyuka 35 daga hannun Gwamna Badaru, inda ya yi Nasarar aiwatar da kaso 33 na bukatun mutanen.

Haka kuma ya ce zai yi duk mai yuwuwa domin kammala sauran ayyuka 2 da suka rage masa, baya ga wanda ya aiwatar a baya.

Gwamnan Jihar ta Jigawa ya bayyana godiyar sa ga mutanen Masarautar Hadejia bisa bashi Lambar girmamawar.

A Jawabinsa, Shugaban Kungiyar Hadejia Ina Mafita Alhaji Baidu Gajo Muhammad Yelleman, ya godewa Gwamna Badaru Abubakar, bisa cika Alkawarirrikan da ya daukawa Al’umma.

Shima a Jawabinsa, Darakta Janar na Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA) Malam Kashifu Inuwa Abdullahi, ya godewa Gwamnan bisa yadda yake hulda da Jama’a.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: