Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar a jiya ya rantsar da Alhaji Sagir Ahmad a matsayin sabon kwamishinan filaye da raya birane.

Gwamnan ya kuma yi kira ga sabon Kwamishinan da ya kasance mai gabatar da aiki bisa gaskiya da rikon amana kuma ya sa Allah a ransa.

Alhaji Sagir Ahmad wanda Gwamanan ya nada domin ya yi aiki a matsayin Kwamishinan filaye ana tsammanin zai kawo sabbin tsare tsare na zamani da zasu kawo cigaba a ma’aikatar.

Tun a baya ya nuna cewar daidai yake da aikin da aka rataya a wuyan nasa domin kuwa ya amsa dukkannin tambayoyin da aka yi masa a zauren majalisar jiha yayin da ake tantanceshi.

Mataimaki na musamman ga Gwamnan Jihar Jigawa a Kafafan Sadarwar zamani Auwal D Sanara (FICA) ya wallafa a shafinsa na facebook.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: