Gwamna Badaru Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Gona Da Wasu Masu Masa Hidima Guda 4

0 76

GWAMNA BADARU YA RANTSAR DA SABON KWAMISHINAN GONA DA WASU MASU MASA HIDIMA GUDA 4
Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar MON, mni ya rantsar da sabon kwamishina da sabbin masu masa hidima guda hudu. Haka zalika, ya bukaci sabbin wadanda aka nada su gudanar da ayyukansu cikin adalci da kwarewa.
An rantsar da Alhaji Auwal Danladi Sankara a matsayin kwamishinan ayyuka na musamman kuma ana sa ran zai kula da ma’aikatar noma ta jihar Jigawa.
Kamar yadda aka sanar “sauran mashawarta na musamman da aka rantsar sun hada da Alhaji Ahmad Garba MK kan harkokin siyasa, Alhaji Bala Sule Kika mai ba da shawara kan harkokin noma, Alhaji Garba Aliyu mai ba da shawara na musamman, da Alhaji Ayuba Magaji Ayuba”.

Leave a Reply

%d bloggers like this: