Gwamna Badaru ya yaba da kokarin kamfanin saye da sarrafa ridi na WACOT bisa samar da gona mai fadin kadada 500 ta noman ridi

0 127

Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar ya yaba da kokarin kamfanin saye da sarrafa ridi na WACOT bisa samar da gona mai fadin kadada 500 ta noman ridi da kuma sashin horas da manoma dabarun noman ridi na zamani.

Gwamnan yayi wannan yabon ne lokacin da ya kai ziyara gonar a garin Gumel.

Muhammadu Badaru Abubakar wanda ya zagaya sassa daban-daban na gonar, ya ce gonar zata samar da ayyukan yi ga matasa a yankin.

Tun farko shugaban kamfanin WACOT, Faruq Bashir Muhammad Gumel, ya ce ya samar da gonar ne domin marawa Gwamnatin tarayya da ta Jihar Jigawa baya bisa kokarin su na fadada hanyoyin tattalin arziki ta fannin aikin gona.

Ya godewa Gwamna Badaru Abubakar bisa goyon baya da kwarin gwiwa da ya bayar na ganin gonar ta tabbata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: