Gwamna Badaru ya yabawa shugaban kasa Buhari bisa yadda yake mulkin sa kan adalci

0 33

Kwamitin shirya zaben babban taron jamiyyar APC na kasa ya yabawa shugaban kasa Muhammad Buhari da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar wajen sawwakawa ayyukan kwamitin a lokacin babban taron jamiyyar na kasa da aka gudanar a Abuja.

Shugaban kwamitin kuma gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, wanda ya bayyana hakan a birnin Abuja, yace sanya bakin shugaban kasa da kuma dattawan jamiyyar ya basu damar yin maslaha da kuma yin zabe a wasu mukamai.

Muhammad Badaru Abubakar, yace hakan ya nuna a fili karamci da dattako da kuma abin misali da ‘yan takarar suka nuna a lokacin babban taron wanda ya nuna cewar sun nuna kishin jamiyya fiye da na son rai.

Shugaban kwamitin ya kuma godewa wakilan kwamitin da jami’an tsaro da shugabanni da magoya baya bisa gudunmawar da suka bayar wajen samun nasarar babban taron.

Leave a Reply

%d bloggers like this: