Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya ce gwamnatin jihar ta dogara da wata doka wajen ba wa mazauna jihar umarnin mallakar makamai domin kare kansu

0 73

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya ce gwamnatin jihar ta dogara da wata doka wajen ba wa mazauna jihar umarnin mallakar makamai domin kare kansu.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan, Jamilu Magaji, ya rabawa manema labarai jiya a Gusau, babban birnin jihar.

Jamilu Magaji ya bayyana cewa gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kaddamar da wasu kwamitocin tsaro a Gusau.

Sanarwar ta bayyana cewa umarnin gwamnan wani bangare ne na kokarin gwamnati na magance matsalolin tsaro da suka dade a jihar.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar tana sane da rashin jin dadin da wasu mutane suna bayyana dangane da sabon matakin.

An yi nuni da cewa, an dauki matakin ne don karfafawa al’ummar da ke fama da tashin hankali sanadiyyar hare-haren da ‘yan fashin daji ke kaiwa, domin samun makaman kare kawunansu da al’ummarsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: