Gwamna Ganduje ya amince da korar wasu ma’aikata 4 na ofishin kula da filaye na jihar Kano daga aiki bisa samun su da laifin cin hanci da rashawa

0 86

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a jiya ya amince da korar wasu ma’aikata 4 na ofishin kula da filaye na jihar daga aiki bisa samun su da laifin cin hanci da rashawa.

Gwamnan ya ce an kama jami’in ne da laifin sayar da kadarorin jama’a, da buga jabun takardu da bayar da bayanan karya da kuma karya bayanan hukuma.

Wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba ya sanyawa hannu, ta bayyana sunayen jami’an da aka kora da Abdulmuminu Usman Magami da Abdullahi Nuhu-Idris da Audu Abba Aliyu da kuma Baba Audu.

Muhammad Garba ya ce an kori jami’an ne bisa shawarar kwamitin bincike da gwamnatin jihar ta kafa wanda ya same su da aikata laifukan.

A wani labarin kuma, kamfanin Air Peace, ya tabbatar wa abokan huldar sa cewa aikin sa ba ya fuskantar wata barazana a Kano duk da rashin fahimtar juna da aka samu a makon jiya tsakaninsa da majalisar masarautar birnin.

Da yake tattaunawa da manema labarai, kakakin kamfanin Air Peace ya ce aikinsu yana tafiya ba tare da wata matsala ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: