Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa sama da yara miliyan 3 da dubu dari 6 ne za’ayi musu rigakafin Polio a makon gangamin lafiyar yara da kuma yaran da ake Haifa a wannan watan na Janairu.

Gunduje ya bayyana hakan ne a lokacin dayake kaddamar da OBR1 da na lafiyar Yara a karamar hukumar Ungoggo dake jihar.

Mataimakin gwamnan Dr. Nasiru Yusuf ne ya bayyana hakan a lokacin daya wakilcin gwamnan kanon, inda ya kara da cewa, gwamnati ta kammala shirye-shirye domin samar da lafiya mai dorewa ga dukkanin al’ummar jihar.

Gwamnatin jihar ta kuma yabawa gwamnatin tarayya, karamar hukumar Ungogo da kuma masarautar Kano, bisa namjin kokarin da sukeyi wajan yaki da cuttuttuka a cikin al’umm.

Ta kuma bukace su akan su sanya ido domin ganin wannan shirin ya dore tare da samun nasara.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: