Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa Alaramma Ahmed Sulaiman kwamishina na biyu a hukumar kula da makarantun firamare ta jihar Kano.

Alaramma Ahmad Sulaiman ne ya tabbatar da ba shi wannan muƙamin a saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook inda ya yi godiya ga gwamnan.

Ya wallafa hotunansa tare da gwamnan, a gefe akwai Sheikh Abdullahi Balalau wanda shi ne shugaban Ƙungiyar Izala, da kuma sakataren ƙungiyar na ƙasa Sheikh Kabir Gombe.

Malam Ahmad Sulaiman ya roƙi Allah ya sa albarka a kujerar da ya samu da kuma roƙon addu’ar jama’a kan taya sa riƙo.

BBCHausa

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: