Gwamna Mai Mala Buni na Yobe ya bude kwalejin kimiyya da fasaha ta Ma’arif da ke Potiskum a karamar hukumar Potiskum

0 93

Gwamna Mai Mala Buni na Yobe ya bude kwalejin kimiyya da fasaha ta Ma’arif da ke Potiskum a karamar hukumar Potiskum.

Da yake jawabi a wajen kaddamarwar, Gwamna Buni ya yi kira ga masu makarantar da su fitar da kudin makaranta mai sauki.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Idi Gubana, ya bukaci mahukuntan kwalejin da su bi ka’idojin amincewa da kuma yin aiki kafada da kafada da ma’aikatar lafiya da ayyukan jin kai ta jihar.

Gwamna Buni ya kuma yi kira ga sauran masu hannu da shuni da su yi koyi da masu makarantar ta hanyar saka hannun jari a fannin ilimi domin habaka cigaban fannin.

A nasa jawabin, Daraktan Kwalejin kuma Mataimakin Shugaban Hukumar Daraktoci na Kwalejin, Sheikh Ibrahim Rijiyan-Lemo, ya ce an kafa kwalejin ne a Potiskum domin kara kaimi ga kokarin gwamnati na sake tsugunar da ‘yan gudun hijira.

Leave a Reply

%d bloggers like this: