Gwamna Mallam Umar Namadi da wasu gwamnonin Arewacin Najeriya 9 za su halarci babban taro kan zaman lafiya na ƙasar Amurka

0 144

Gwamna Mallam Umar Namadi da wasu takwarorinsa gwamnonin Arewacin Najeriya 9 za su halarci babban taro kan zaman lafiya na ƙasar Amurka.

Taron wanda wanda cibiyar wanzar da zaman lafiya ta ƙasar Amurka wato (USIP) ta shirya, za a gudanar da shi ne a ranar Talata 23-04-2024.
Taken taron na bana shine “Ci gaban kwanciyar hankali a Arewacin Najeriya”.

Ganawa da gwamnonin na da nufin ƙoƙarin samo bakin zaren matsalar taɓarɓarewar tsaro da Najeriya ke fuskanta, tareda zufafa binciken yadda za a tsamo da kitse daga wuta.

A wata sanarwa da cibiyar ta USIP ta wallafa a shafinta na yanar gizo, ta ce; tattaunawar za ta samar da wata kafa da gwamnonin jihohin Jigawa, Katsina, Katsina, Zamfara, Kaduna, Niger, Sokoto, Kebbi, Kano da Plateau domin bayyana ra’ayoyinsu kan ƙalubalen da jihohinsu ke fuskanta.

Har ila yau, taron zai yi nazari kan irin cigaban da yankin Arewacin Najeriya da ma ƙasar zai yi ta dalilin wanzuwar zaman lafiya.

Gwamna Namadi zai kasance ɗaya daga cikin masu tattaunawar tareda wasu takwarorinsa na Arewacin Najeriya, wanda Ambasada Johnnie Carson babban mai bada shawara kan Afrika na cibiyar ta USIP ne zai jagorancin taron.

Ana sa ran taron zai samar da fahimtar juna na hanyoyin da za a bi domin samun zaman lafiya da ingantaccen tsaro mai ɗorewa a yankin Arewacin Najeriya. La’akkari da yadda ƙalubalan dake da nasaba da masu tada ƙayar baya, ƙabilanci ke kawo babban cikas wajen ɗorewar zaman lafiya da bunƙasar tattalin arziƙi a yankin.

-Government House Media Office 

Leave a Reply

%d bloggers like this: