Gwamna Matawalle Ya Bukaci EFCC Ta Bibiyi Wasu Jami’an Gwamnatin Tarayya Masu Barin Gado

0 60

Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara ya bukaci Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) da ta bibiyi jami’an fadar shugaban kasa da ‘yan majalisar zartaswar na tarayya masu barin gado.

Bello Matawalle ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani ga wata sanarwa daga Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, dake cewa Hukumar EFCC ta aike da goron gayyata ga dukkan gwamnoni da kwamishinoni masu barin gado a yunkurin fara bincike.

Ya ce bai kamata irin wannan binciken ya tsaya kan gwamnoni da kwamishinoni masu barin gado ba, har da wadanda ke aiki a fadar shugaban kasa.

Bello Matawalle ya kuma bukaci shugaban hukumar na EFCC da ya tabbatar da cewa bai sanya siyasa a binciken ba, sannan kuma a gurfanar da duk wadanda aka samu da hannu a almundahana a gaban kuliya.

A halin da ake ciki, Gwamnatin Tarayyar ta ce Gwamnan na jihar Zamfara yana da ‘yancin fadin albarkacin bakinsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: